Allah yasa a sace buhari da El-Rufai

Sheikh Bello Yabo ya yi addu'ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai.
Fitaccen malamin addinin Islama ya caccaki gwamnatin Buhari da mukarraban shugaban kasa.

Bello Yabo ya koka da yadda 'yan Najeriya ke ciki saboda gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro.

A makon da ya gabata ne aka ga wani bidiyon dake nuna lokacin da 'yan bindiga ke barazanar sace shugaban kasa Buhari.

Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Sokoto, Bello Yabo, yayi addu'ar Allah ya hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu da 'yan ta'adda.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post