Duniya Zata Wargaje Saboda makaman nukilyar MDD

Duniya na dab da hadarin wargajewa saboda makaman nukiliya - MDD

Mista Guterres ya yi gargadin duniya na daf da fadawa yakin nukiliyaImage caption: Mista Guterres ya yi gargadin duniya na daf da fadawa yakin nukiliya
Shugaban majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa duniya na fuskantar gagarumin hadarin makaman nukiliya fiye da kowa ne lokaci tun bayan yakin cacar-baka.

Antonio Guterres ya yi wannan gargadi ne a New York, inda ya bukaci shugabanni da su karfafa yarjejeniyar hana bazuwar makaman na kare-dangi.

Babban Sakataren ya ce a yanzu kiris ya rage wa duniya ta rushe gaba daya, inda take bakin hadarin wargazata ta makamin nukiliya.

Haka shi ma Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya maimaita wannan gargadi a kan Koriya ta Arewa da kuma burin Iran na mallakar makaman nukiliya.

Shi kuwa shugaban Rasha Vladimir Putin, ya aika da wasika ne wadda a ciki ya ke jaddada cewa gwamnatinsa tana kan alkawarinta na mutunta yarjejeniyar hana bazuwar makaman nukiliya.

Mista Putin ya ce babu wanda zai yi nasara a yakin nukiliya.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post