Shugaban da yafi kowa gaskiya a Tarihin Nigeria

Dalilin dayasa marigayi Ummaru Musa Yar Adua yazama shugaba mafi gaskiya da adalci a tarihin nigeria shine:

A watan april na shekarar 2007 ana daf da gudanar da zaben shugaban kasa, marigayi Ummaru Musa yar Adua yakira dukkan shugabannin tsaron kasar nigeria yayi meeting dasu (Yan Sanda, Sojan Sama, Sojan Kasa, Kwastam, Hukumar zabe INEC, kowanne kaki na wannan kasar yana gurin, yake gayamusu cewa;

Kada wanda yayi magudin zabe da kuri’a daya, sannan duk wanda yaci zabe tsakani da Allah abashi ko musulmi ko Christa, ko daga arewa ko daga kudu, ko daga wace jam’iyya yafito.

Mutane su zama masu adalci da gaskiya, wannan kasar tamu nigeria adalci da gaskiya kadai ke iya gyarata, karfin mulki ko bindiga baya kawo gyara acikin al’umma.

Idan kuma kuka sake akayi magudin zabe idan nagano gaskiya koda an rantsar dani amatsayin zababben shugaban kasar nigeria zan sauka har sai idan an sake zaben gaskiya.

Wannan maganar da marigayi Ummaru Musa Yar Adua yayi sai da Obasanjo yaso Ya Sauya Shi Amatsayin dan takara a karkashin jam’iyyar PDP.

Allah ya gafarta wa Ummaru Musa Yar Adua. 🙏
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post