Morocco ta cinye Nigeria a bugun daga Kai sai Mai tsaron raga

Kwallon Kafa : Kungiyar Kwallon Kafa ta mata ta Najeriya ta yi rashin nasara.

Kungiyar Kwallon kafa ta kasar Morocco Atlas Lionesses ta cinye Najeriya a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Najeriya ta buga wasan ne da yan wasa tara, sakamakon jajayen katina guda biyu da ta samu.

An tashi wasan 1-1, inda bayan an cinye Karin lokaci aka tafi bugun daga ke sai mai tsaron raga, inda Morocco ta cinye duka bugun guda 5, sai dai Najeriya ta barar da guda 1.

Kasar Morocco ta cancanci buga wasan karshe, inda za ta fafata da kasar Afirika ta Kudu.
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post