gaskine Ana Zinace Zinace Kungiyar Shi'A AlZakZaky

Gaskiya Ne Ana Zinace-Zinace A Ƙungiyar Shi'a (IMN) - Khadijah Mustapha Tsohuwar Ɗalibar Zakzaky



Sunana Khadijah Mustapha kuma ni 'yar asalin jihar Kaduna ce a ƙaramar Hukumar Giwa, sannan na yi tafiyar kungiyar Shi'a ta IMN karkashin Ibrahim Zakzaky tun daga shekarar 1990 - 2013.

Akwai maganganu da ake yawan yi akan neman Mata da fasikanci dasu a tsakanin mabiya Zakzaky a tsawon lokaci da ya haifar da surutai har wasu na ganin cewa karya ko sharri ake musu.

Ni da nake wannan rubutu Khadijah Mustapha cikakkiyar shaida ce akan haka domin ni 'yar cikin gida ce tsawon shekaru kafin Allah ya tsamar da ni daga wannan mummunan hanya ta ɓata da hallaka na wayi gari a yau a matsayin Musulma Ahlul Sunnah!

Abin da ya ja hankali na har na yi wannan rubutun shi ne, na ga rubutu da wani yaro Matashi ɗan Shi'a mai suna Abdulhadi Aminu ya rubuta, yana nuna baƙin ciki da takaici akan yadda Zinace-Zinace ke ƙaruwa a tafarkin Zakzaky.

Daga baya Yaron ya janye rubutun da ya yi sannan ya sake wani rubutun yana korafin an sauya akalar maganarshi zuwa wani wuri.

Na ba shi uzuri kasancewar Yaro ne bai san dawar garin ba, kuma ina kyautata zaton an yi mishi mazurai ne har ya ɗauki matakin da ya ɗauka na janye rubutun..

"Ina faɗi da babbar murya kowa ya sani fasadi da Mata a wurin Malaman Shi'a wannan ba komai bane! Matan dake Shi'a sun san haka muddin za su fadi gaskiya, da yawa sun bar Shi'a saboda wannan matsalar".

Daga Shafin datty Assalafy
Post a Comment (0)
Previous Post Next Post